Isa ga babban shafi

Hare-haren Isra'ila sun raba Falasdinawa dubu dari 3 da 38 da matsugunansu a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari 3 da 38 ne luguden wutar da Isra’ila ke ci gaba da yi a kan Gaza ya tilasta musu barin gidajensu, a  yayin da a gefe guda mahukuntan yankin suka ce adadin wadanda suka mutu a bangarensu ya kai dubu 1 da dari 2. 

Dubun dubatar mutane ke ci gaba da tserewa daga gidajensu a Gaza sakamakon yadda Isra'ila ke ci gaba da ruwan wuta kan fararen hula.
Dubun dubatar mutane ke ci gaba da tserewa daga gidajensu a Gaza sakamakon yadda Isra'ila ke ci gaba da ruwan wuta kan fararen hula. AP - Fatima Shbair
Talla

A wata sanarwar hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa daren jiya Laraba, adadin wadanda luguden wutar Isra’ila ya daidaita a yankin Gaza ya karu da kimanin mutane dubu 75, daga wanda ta bayar tun da farko, inda a yanzu adadin ya kai dubu dari 3 da 38 da dari 9 da 34. 

Cikin wadanda Isra'ila ta kashe har da tarin kananan yara a yankin na Gaza baya ga dattijai.
Cikin wadanda Isra'ila ta kashe har da tarin kananan yara a yankin na Gaza baya ga dattijai. AFP - EYAD AL-BABA

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da luguden wuta a kan wuraren da take ganin sansanonin mayakan kungiyar Hamas ne a yankin na Gaza, yankin da ke da yawan al’umma miliyan 2 da dubu dari 3, a matsayin martani ga hari mai ban mamaki da Hamas ta shammace ta da shi a ranar Asabar. 

A bangare guda alkaluman wadanda suka mutu a yakin na Hamas da Isra’ila, bangaren yahudawa akwai mutane dubu 1 da 200 galibi fararen hula baya ga sojoji kusan 200 sai kuma a harin mafi muni da Isra’ilan yahudu ta taba fuskanta a tarihi. 

A bangaren Gaza kuwa ma’aikatar lafiyar yankin ta ce adadin wadanda suka mutun ya kusa dubu 1 da 200 lura da yadda Sojin Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a lungu da sako na birnin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.