Isa ga babban shafi

MDD ta bayyana damuwa game da ficewar rundunar Monusco a Jamhuriyar Congo

Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun bayyana rashin jin dadinsu kan kiran da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ta yi na a gaggauta janye dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato Monusco yayin wani aikin sintiri a yankin Munigi mai tazarar kilomita 8 daga Goma da ke gabashin Congo, ranar 19 ga watan yuli, 2013.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato Monusco yayin wani aikin sintiri a yankin Munigi mai tazarar kilomita 8 daga Goma da ke gabashin Congo, ranar 19 ga watan yuli, 2013. © AFP
Talla

A makon da ya gabata ne shugaban kasar Congo, Felix Tshisekedi, ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta gaggauta janye tawagar wanzar da zaman lafiya ta Monusco da ta shafe kusan shekaru 25 tana aiki a kasar da ke tsakiyar Afirka .

Shugaban dai ya bukaci janyewar dakarun ne daga karshen wannan shekarar, maimakon Disambar 2024 kamar yadda aka tsara tun da fari.

Kwamitin Sulhun na bukatar sabunta wa'adin Monusco a watan Disamba, inda gwamnatin Kinshasa ta nuna shakku kan tasirin rundunar, musamman wajen kare fararen hula daga tashe-tashen hankula daga masu tayar da kayar baya, da aka debe shekaru da dama ana fama da su.

Yayin da har yanzu yanayin tsaro ke cikin halin ha’ula’i a yankin gabashin kasar, Majalisar Dinkin Duniya ta nuna shakku game da shawarar gaggauta mika aikin wanzar da zaman lafiya ga sojojin Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.