Isa ga babban shafi

Sojin Congo sun kashe mutane 48 da ke adawa da zaman dakarun MDD a Goma

Akalla mutane 48 aka tabbatar da sun mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a wani sumame da Sojojin jamhuriyyar Demokradiyyar Congo suka kai kan wata kungiyar addini da ke adawa da ci gaba da kasancewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Goma.

Dakarun Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Dakarun Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. © AFP
Talla

Alkaluman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara a jiya Alhamis bayan tattaunawa da shaidu a yankin da sumamen ya faru, shaidun gani da ido sun tabbatar da kisan fiye da mutane 48 a guda cikin sumamen da Sojojin suka kaddamar kan mambobin kungiyar.

Tun farko kungiyar ta mabiya addinin Kirista ta shirya gudanar da wani gangami ne don nuna adawa da ci gaba da kasancewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a birnin na Goma.

Rahotanni sun ce dakarun na Congo sun kai sumamen wuraren bauta da kuma gidan Radio inda mambobin kungiyar ke gabatar da shirin kalubalantar kasancewar dakarun a kasar, inda suka kashe mutane 10.

Alkaluman sojojin kasar da AFP ya samu gani, ya nuna yadda mabanbantan sumame kan kungiyar addini ya kashe mutane 48 baya ga jikkata wasu 75.

Rahotanni daga wata majiyar Sojin na Congo sun tabbatar da yadda dakarun kasar suka kwace tarin makamai daga hannun mambobin kungiyar tare da kame wasu mutum 168 da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.