Isa ga babban shafi

MDD ta yi gargadi game da tabarbarewar ayyukan jin kai a Jamhuriyar Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargaba kan tabarbarewar ayyukan jin kai a larduna uku na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda kusan mutane miliyan 3.3 suka rasa matsugunansu tun daga watan Maris din shekarar 2022.

Fusatattun mutane a Congo kenan, lokacin da suka kai hari ofishin MDD da ke Goma a ranar 26 ga watan Yulin 2022.
Fusatattun mutane a Congo kenan, lokacin da suka kai hari ofishin MDD da ke Goma a ranar 26 ga watan Yulin 2022. AFP - MICHEL LUNANGA
Talla

'Yan bindiga da kungiyoyin 'yan tawaye sun addabi yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo tsawon shekaru da dama, tun bayan barkewar rikici a yankin a shekarar 1990.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, domin samun damar biyan bukatun mutanen da tashe-tashen hankula a yankin ya shafa, ma'aikatan jin kai na bukatar sama da dala biliyan 1.5 wajen taimaka musu.

'Yan tawayen M23 sun kwace ikon da dama daga cikin arewacin Kivu, tun daga lokacin da suka dauki makamai a karshen shekarar 2021, bayan shekaru su na kai hare-hare a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.