Isa ga babban shafi

'Yan tawayen ADF sun kashe fararen hula 30 a Jamhuriyar Congo- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutane 30 mayakan ‘yan tawayen ADF da ke biyayya ga kungiyar IS suka kashe a jamhuriyyar Demokradiyyar Congo cikin makon nan kadai.

Mayakan 'yan tawayen ADF.
Mayakan 'yan tawayen ADF. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

Kungiyar ta ADF da ta fara kafuwa a Uganda gabanin gangarawa Congo tare da samun matsuguni a gabashin kasar tun a shekarun 1990 ta na fuskantar jerin zarge-zargen kisan tarin fararen hula.

Sanarwar da Majalisar dinkin duniyar ta fitar a yammacin jiya alhamis ta ce tsakanin ranakun Lahadi da litinin din da suka gabata ne ‘yan tawayen na ADF suka aikata kisan a garuruwan Mambasa da Irumu da ke kan iyaka.

Shirin Majalisar kan rikicin kasar ta Congo da aka fi sani da Monusco da ke fitar da alkaluman kisan, ya yi tir da hare-haren na ADF wanda ya ce ya na ci gaba da tagayyara rayuwar al’ummar yankin.

Shugabar shirin na Monusco, Bintou Keita ta ce abin takaici ne yadda ‘yan tawayen ke ci gaba da kisan fararen hular da basu ji ba basu gani ba, ta na mai kira ga mahukunta Congo kan su gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu a makamantan hare-haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.