Isa ga babban shafi

MDD ta zargi 'yan tawayen M23 da aikata muggan laifuka da cin zarafi a Congo

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya zargi mayakan kungiyar ‘yan tawayen M23 da aikata manyan laifuka baya ga azabtarwa da kuma cin zarafin mata a yankin gabashin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

A shekarar 2021 ne M23 ta dawo da hare-hare tare da kashe-kashen fararen hula baya ga yiwa tarin mata Fyade.
A shekarar 2021 ne M23 ta dawo da hare-hare tare da kashe-kashen fararen hula baya ga yiwa tarin mata Fyade. AFP - GUERCHOM NDEBO
Talla

Cikin rahoton na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke zuwa bayan ziyarar da kwararru na musamman suka kai yankin Rutshuru guda cikin sassan da ‘yan tawayen na M23 ke iko da shi a lardin arewacin Kivu na Congo ya bayyana yadda kwararan hujjoji ken una irin ta’annatin da ‘yan tawayen ke aikatawa ta hanyar azabtarwa da cin zarafin mata baya ga kisa da kuma garkuwa da tarin matasa da nufin hanasu shiga aikin sa kai don taimakawa dakarun gwamnatin kasar.

Rahoton mai shafuka 21 da MDD ta fitar a makon nan bayan tattauna da daidaikun mutane da ya kai ga tattara bayanai daga majiyoyi fiye da 230 ya koka da irin laifukan da ‘yan tawayen na M23 ke aikatawa a yankunan da suka kwace iko da su a gabashin kasar.

Gomman shekaru kenan yankin arewacin Congo na fama da rikici inda kungiyoyi masu dauke da makamai fiye da 120 ke fada kodai a tsakaninsu da dakarun gwamnati ko kuma tsakanin wani bangare da wani bangare.

M23 guda cikin irin wadannan kungiyoyi, shekaru 10 da suka gabata ne duniya ta san da karfinta bayan da mayakanta suka kwace iko da birnin Goma da ke makwabtaka da Rwanda, sai dai a 2021 ne suka dawo da hare-hare inda suka bi sahun sauran kungiyoyi wajen kashe-kashen fararen hula baya ga yiwa tarin mata Fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.