Isa ga babban shafi

Kisan da ake a Jamhuriyar Congo ya yi kamari - MDD

Majalisar dinkin duniya ta koka game da karuwar rikicin gabashin jamhuriyar dimokradiyyar Congo, inda ta ce kawo yanzu rikicin ya tafi da rayukan mutane fiye da 1,300 ciki har da kananan yara fiye da 100. 

Kwamandojin URDPC/CODECO kenan, lokacin da ssuke ratsa kauyen Linga da ke gundumar Ituri, na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo. An dauki hoton ranar 13 ga Janairu, 2022.
Kwamandojin URDPC/CODECO kenan, lokacin da ssuke ratsa kauyen Linga da ke gundumar Ituri, na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo. An dauki hoton ranar 13 ga Janairu, 2022. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

 

Ko da yake karin bayani shugaban hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya, Volker Turk, ya yi gargadin cewa har yanzu ana ci gaba da kisan jama’a da keta hakkin su a yankunan kasar, musamman yankin Ituri da arewacin Kivu na kasar. 

Kungiyoyin ADF da CODECO da M23 da Zaire da Nyatura ne cikin kungiyoyi mafiya hadari da ke kisan jama’a ba ji ba gani a yankin, da kuma jefa rayukan jama’a cikin hadari matuka da gaske. 

Majalisar dinkin duniya ta ce daga watan Oktoban 2022 zuwa yanzu rikicin yankin ya hallaka mutane sama da 1,334, da kuma kananan yara 104. 

Turk ya kuma ce yakin ya raba mutane miliyan 6 da muhallan su, abinda ke zama yakin da ya raba mutane mafi yawa da muhallan su a nahiyar Africa.  

Ya kuma yi gargadin cewa har yanzu wannan yankin na cikin tashin hankali yayin da al’amarin ke barazanar yaduwa zuwa wasu sassan kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.