Magatakardan MDD yana Burundi don nemo mafita a game da rikicin Congo
Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya sauka a kasar Burundi, inda ya tattauna da shugaban kasar a game da rikicin da ake a makwafciyarta, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Wallafawa ranar:
A yayin ziyarsa ta farko a kasar, Guterres ya yi kira ga kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar da su ajiye makaman, kana ya ce dole ne a zage dantsi wajen kawo karshen rikicin da ake yi kasar.
Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na da dimbim arzikin karkashin kasa, wanda ake matukar nema a sassan duniya, lamarin da ake ganin ya kwadaita wa wasu kungiyoyi daukar makamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu