Isa ga babban shafi

Shugaban Congo ya bukaci ficewar dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar

Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyya Congo ya yi kira da a gaggauta janye dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a kasar yau  kusan shekaru 25 kenan. 

Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, FelixTshisekedi a yayin wata ziyara da ya kai birnin Berlin na Jamus.  15 ga Nuwamban,2019.
Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, FelixTshisekedi a yayin wata ziyara da ya kai birnin Berlin na Jamus. 15 ga Nuwamban,2019. Photo: Tobias schwarz/AFP
Talla

Felix Tshisekedi  ya shaida wa taron Majalisar Dinkin Duniyar cewa lokaci ya yi da kasarsa za ta dauki ragamar gyarar makomarta. 

Ya ce zaman dakarun kiyaye zaman lafiya su kimanin dubu  15 bai kawo karshen matsalolin da ake samu a kasar da rikice-rikice suka wa katutu ba, zalika, bai taimaka wajen kare rayukan fararen hula ba. 

Batun janyewar wadannan dakaru na Majalisar Dinkin Duniya ne ya mamaye duk wata  muhawwar a Congo tsawon shekaru, kana ya kasance abin da ke janyo tankiya a kasar da ke yankin Tsakiyar Afrika.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kungiyoyi masu dauke da makamai sama da 100 ne ke gabashin kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, wadanda ke kashe mutane tare da aikata manyan laifuka dabam-dabam da sukaa hada da cin zarafin bil adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.