Isa ga babban shafi

Congo ta cafke manyan sojojinta bayan mutuwar mutane 50

Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo ta cafke wasu manyan sojojinta bayan kusan mutane 50 sun mutu a wata zanga-zangar adawa da Majalisar Dinkin Duniya a yankin gabashin kasar.

Wasu daga cikin sojojin a yankin Goma da ke Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.
Wasu daga cikin sojojin a yankin Goma da ke Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

A makon jiya ne sojojin Congo suka hana dandazon mabiya wani addini gudanar da zanga-zangar ta nuna adawa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a birnin Goma, inda jami'an tsaro suka murkushe masu boren.

Wata takardar sirri ta rundunar sojin kasar da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya gani, sannan jami'an tsaro suka tabbatar da ingancinta, ta bayyana cewa, mutane 48 ne suka mutu a jumulce da suka hada da jami'an 'yan sanda da masu boren suka kashe su.

A  Litinin din nan ne, Ministan Cikin Gidan Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo, Peter Kazadi ya bayyana cewa, daga cikin sojojin da aka tsare har da wasu manyan kwamandojin kasar guda biyu, kuma nan kusa za a soma yi musu shari'a.

Ministan ya yi balaguro zuwa birnin na Goma domin gane wa idanunsa abin da ya faru tare da gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ya samu rakiyar Ministan Tsaron kasar, Jean-Pierre Bemba.

Mun binciki daukacin manyan jami'an soji a birnin Goma, kuma tuni aka tura wasu daga cikinsu ofishin masu shigar da kara na soji don fara tuhumar su. Inji Kazadi.

Ministan ya bukaci al'umma da su kwantar da hankalinsu tare da mara wa gwamnati baya don ganin ta yi adalci a wannan shari'ar.

Tuni kungiyar kare hakkin bil'adama ta LUCHA ta yi madalla da tsare sojojin, amma ta yi kira da a cafke hatta Magajin Birnin Goma da gwamnan Arewacin Kivu.

Kimanin shekaru 30 kenan da 'yan tawaye ke cin karensu babu babbaka a yankin gabashin Jamhuriyar  Dimokuradiyar Congo, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke zuba akalla dala biliyan 1 a kowacce shekara a yankin don samar da zaman lafiya. 

Sai dai akwai mutane da dama daga yankin da ke zargin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen wanzar da zaman lafiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.