Isa ga babban shafi

Nijar ta haramta wa jiragen Faransa shawagi a sararin samaniyarta

Gwamnatin sojin Nijar, ta ce tana maraba da dukkanin jiragen kasuwanci da za su gifta ta cikin kasarta, sai dai ta haramta wa jiragen Faransa har ma da jiragen da kasar ke daukar hayarsu ratsawa ta kasar.

Jirgin Air France na kasar Faransa.
Jirgin Air France na kasar Faransa. REUTERS - Regis Duvignau
Talla

Sa'o'i kadan kafin Faransa ta sanar da janye jakadanta da sojojinta daga Nijar, mahukuntan sojin kasar sun ce, an rufe sararin samaniya ga jiragen Faransa.

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama a Afirka da Madagascar (Asecna) ta ce sararin samaniyar Nijar a bude take ga dukkanin jiragen kasuwanci na kasa da kasa, amma ban da jiragen Faransa ko wanda kasar ta yi hayar su ciki har da na Air France.

Nijar ta kuma haramta ratsawar duk wani jirgin soji da ya fito daga kowace kasa ta sararin samaniyarta ba tare da izini ba.

Dangantaka tsakanin Faransa da Nijar ta tabarbare ne tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a wani juyin mulki da aka yi ranar 26 ga watan Yuli.

Faransa na goyon bayan ECOWAS don ladabtar da Nijar

Faransa ta goyi bayan Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS, wadda ta yi barazanar daukar matakin soji don dawo da Bazoum kan karagar mulki, abin da ya sanya gwamnatin sojin Nijar daukar matakin rufe sararain samaniyar kasar a ranar 4 ga watan Agusta, saboda barazanar shiga tsakani da take fuskanta daga kasashe makwabta.

Kusan wata guda kenan da Nijar ta sake bude sararin samaniyarta ga jiragen kasuwanci, kafin ta sanar a ranar Lahadi cewa jiragen Faransa an haramta musu yin shawagi a cikin kasar.

Kamfanin na Air France wanda ya dakatar da zirga-zirgar jiragensa zuwa Nijar a ranar 7 ga watan Agusta, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran AFP cewa ya dakatar da yin shawagi a sararin samaniyar Nijar.

Air France na cikin manyan jiragen duniya masu zirga-zirga zuwa nahiyar Afrika.
Air France na cikin manyan jiragen duniya masu zirga-zirga zuwa nahiyar Afrika. © Annie Risemberg / AFP

A matsayinsa na babban kamfanin jirgin da ke zirga-zirga daga nahiyar Turai zuwa Afirka, Air France a yanzu ba zai iya shawagi a sararin samaniyar yankin Sahel ba, yayin da aka rufe sararin samaniyar Libiya da Sudan saboda rikice-rikce, da kuma matsalar tsaro da ke kara kamari a kasar Mali, lamarin da ya tilasta wa jiragen sama yin zagaye ta tekun Bahar Rum zuwa gabas, ko kuma yammacin gabar tekun Afirka da kuma Morocco da Aljeriya.

A halin da ake ciki kuma, iyakokin Benin da Najeriya na ci gaba da kasancewa a rufe tun bayan da Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta haramta alakar kasuwanci da Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.