Isa ga babban shafi

Faransa za ta janye jakada da kuma dakarunta daga Nijar

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana cewa kasar na shirin janye jakadanta a Nijar baya ga ilahirin sojojinta da ke kasar cikin watanni masu zuwa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. via REUTERS - POOL
Talla

A jawabin kai-tsaye da ya gabatar ta gidan talabijin yau Lahadi, shugaba Macron ya bayyana cewa zuwa nan da karshen shekara ne dakarun na Faransa za su kammala ficewa daga kasar.

Takun-saka ta yi karfi ne tsakanin Faransa da Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya hambarar da gwamnatin Bazoum Mohamed.

A cewar Macron nan da sa’o’i kalilan jakadan Faransa da ilahirin jami’an diflomasiyyar kasar da ke Nijar za su kammala dawowa gida wanda ke kawo karshen duk wata hadakar soji tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewa nan da ‘yan kwanaki ko watanni dakarun za su fara dawowa gida amma sai zuwa karshen shekara za su kammala barin kasar ta Nijar.

A martaninta da ta fitar, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bayyana sanarwar ta Macron a matsayin gagarumar nasara ga al'ummar Nijar da ke fatan 'yantar da kasarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.