Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Nijar ta tabbatar da janyewar sojojin Faransa daga kasar

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, ta bayyana sanarwar janye jakada da kuma dakarun Faransa daga kasar a matsayin wata gagarumar nasara a fafutukar da al’umma ke yi don tabbatar da ‘yancin kasar. 

Faransa ta fara tattaunawa da wasu manyan gwamnatin sojin Nijar, game da ficewar dakarunta daga kasar, bayan juyin mulkin watan Yulin 2023.
Faransa ta fara tattaunawa da wasu manyan gwamnatin sojin Nijar, game da ficewar dakarunta daga kasar, bayan juyin mulkin watan Yulin 2023. © THOMAS COEX / AFP
Talla

Hatta ma kungiyoyin fararen hula, wadanda suka jima suna fafutukar neman janye dakarun Faransa, sun bayyana farin cikinsu a game da wannan sanarwa da shugaba Emmanuel Macron ya fitar a ranar Lahadi. 

Wannan matakin ya zo ne bayan kai ruwa rana da aka rika yi tsakanin Faransa da kuma sabuwar gwamnatin sojin Nijar da ta nemi ficewar jakadan kasar da ta taba yi mata mulkin mallaka da kuma dakarunta da ke jibge a kasar.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Baro Arzika. 

Tun da farko, shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana cewa kasar na shirin janye jakadanta a Nijar baya ga ilahirin sojojinta da ke kasar cikin watanni masu zuwa.

A jawabin kai-tsaye da ya gabatar ta gidan talabijin a ranar Lahadi, shugaba Macron ya bayyana cewa zuwa nan da karshen shekara ne dakarun na Faransa za su kammala ficewa daga kasar.

Takun-saka ta yi karfi ne tsakanin Faransa da Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya hambarar da gwamnatin Bazoum Mohamed.

Wasu 'yan Nijar da ke zanga-zangar nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Wasu 'yan Nijar da ke zanga-zangar nuna goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar. © AFP

A cewar Macron nan da sa’o’i kalilan jakadan Faransa da ilahirin jami’an diflomasiyyar kasar da ke Nijar za su kammala dawowa gida wanda ke kawo karshen duk wata hadakar soji tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Macron ya bayyana cewa nan da ‘yan kwanaki ko watanni dakarun za su fara dawowa gida amma sai zuwa karshen shekara za su kammala barin kasar ta Nijar.

A martaninta da ta fitar, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bayyana sanarwar ta Macron a matsayin gagarumar nasara ga al'ummar Nijar da ke fatan 'yantar da kasarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.