EU ta jaddada goyon bayanta ga Jakadan Faransa da ke killace a Nijar
Tarayyar Turai ta, ta bakin jagoran diflomasiyyarta, Josep Borrell ta bayyana goyon bayanta ga jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar, Sylvain Itte, wanda ke fuskantar matsanancin matsin lamba bayan da ya ki bin umurnin da aka ba shi na ficewa daga kasar.
Wallafawa ranar:
Tarayyar Turai ta kuma sabanta goyon bayanta ga Mohamed Bazoum, zababben shugaban Jamhuriyar Nijar da aka hambarar, wanda ke tsare a halin yanzu, tana mai yabawa da jajircewarsa.
Yaki da ta'addanci a Sahel
Borrell ya kuma ce kungiyar Turai ta amince da bukatar sake salo a yakin da ake da ta’addanci a yankin Sahel, wanda Faransa ta jagoranta tsawon shekaru.
A makon da ya gabata, shugaba Emanuel Macron ya ce sojojin da suka yi juyin mulki sun yi garkuwa da jakadan a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Yamai, inda suke ciyar da shi abincin da sojoji ke ci ,bayan da suka hana a sshigo masa da nasa abincin.
Bayan kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed a watan Yuli, sojojin da suka yi wannan aiki sun fusata da yadda tsohuwar uwargijiyar tasu ta ta nuna rashin amincewa da gwamnatinsu, lamarin da ya sa suka kori jakadan Faransa a kasar,
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu