Isa ga babban shafi

Mahsa Amini: Iran ta yanke wa wasu mata biyu hukuncin zaman gidan yari

Wasu ‘yan jarida mata biyu ‘yan kasar Iran za su shafe kusan wata guda a gidan yari a wani bangare na hukuncin dauri na shekaru uku, bisa samunsu da laifin hada baki da yunkurin tayar da tarzoma, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a ranar Lahadi.

Kabarin Mahsa Amini a Iran
Kabarin Mahsa Amini a Iran © RFI persan
Talla

A karkashin hukuncin, Negin Bagheri da Elnaz Mohammadi za su fuskanci kashi daya bisa arba'in na wa'adin, ko kuma kasa da wata guda, a gidan yari, kamar yadda lauyansu Amir Raisian ya shaida wa manema labarai.

Lauyan ya kara da cewa an dakatar da sauran wa’adin ne sama da shekaru biyar, inda a lokacin za a bukaci su karbi horo na musamman kan da’a da kuma haramta musu fita daga kasar.

Raisian bai yi karin haske kan ko za a iya daukaka kara kan hukuncin ba, kuma rahoton bai yi cikakken bayani kan zargin da ake yi wa ‘yan jaridar ba.

'Yar'uwar Mohammadi, Elahe, wacce ke aiki da jaridar Ham Mihan, tun a watan Satumban 2022 take zaman gidan yari bayan da ta bayar da rahoton jana'izar Mahsa Amini, mai shekaru 22, wacce ta mutu a hannun 'yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.