Isa ga babban shafi

Jami'an tsaro sun bude wuta kan masu zanga-zangar cika kwana 40 da kisan Mahsa

Jami’an tsaro a Iran sun bude wuta kan dandazon masu zanga-zangar cika kwanaki 40 da kisan matashiya Mahsa Amini inda mutane da dama suka jikkata, ciki har da wadanda suka yi dafifi a kabarin matashiyar.

Fiye da wata guda ana zanga-zangar wadda ta janyowa Iran karin takunkumai.
Fiye da wata guda ana zanga-zangar wadda ta janyowa Iran karin takunkumai. AFP - JOHN MACDOUGALL
Talla

Dubunnan masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini sun yi dafifi a kabarin matashiyar da ke yankin Saqez don jimamin cika kwanaki 40 da kisan da aka yi mata, duk kuwa da matakan tsaron da gwamnatin kasar ta sanya don hana gangamin a yau laraba.

Baya ga wadanda suka yi dafifi a makabarta da aka birne Mahsa wasu dubunnan masu zanga-zangar na daban sun taru a dandalin Zindan da ke cikin garin na Saqez a yammacin yankin Kurdawa lamarin da ya sanya jami’an tsaro bude wuta tare da amfani da hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa dandazon.

Wani faifan bidiyo da tuni ya fara yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jami’an ‘yan sandan ke amfani da karfin wajen tarwatsa masu zanga-zangar, wanda wata kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Norway da ke sanya idanu a zanga-zangar ta Iran ke cewa matakin da jami’an suka dauka ya take dokokin hakkin masu gangamin.

Dubun-dubatar ‘yan kasar ta Iran galibi mata ne ke ci gaba da zanga-zanga don nuna bacin ransu game da kisan matsahiya Amini mai shekaru 22 kwanaki 3 bayan jami’an tabbatar da da a sun kame ta bisa laifin kin saka hijabi.

Fiye da wata guda ana ci gaba da zanga-zangar a sassan Iran wadda ta samu goyon baya daga kasashe daban-daban yayinda ta janyowa kasar karin takunkumai daga ketare, sai dai gangamin ya sake karfafa a yau ne dai dai lokacin da ake kammala makokin kwanaki 40 da bisa al’ada ake yiwa kowanne mamaci a Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.