Isa ga babban shafi

Sama da mutum 80 ne suka mutu a zanga-zangar Iran - Amnesty International

Jami'an tsaron kasar Iran sun kashe mutane sama da 80 a birnin Zahedan da ke kudu maso gabashin lardin Sistan-Baluchestan, a wani mataki na murkushe masu zanga-zangar da aka yi a kasar, kamar yadda masu rajin kare hakkin bil'adama suka yi zargin.

Masu zanga-zanga a Iran kan mutuwar budurwa Mahsa Amini a hannun 'yan sanda.
Masu zanga-zanga a Iran kan mutuwar budurwa Mahsa Amini a hannun 'yan sanda. AP
Talla

Shugaba Ebrahim Raisi ya ba da umarnin gudanar da bincike kan tarzomar da ta fara tun ranar 30 ga watan Satumba bayan sallar Juma'a, wanda hukumomi suka bayyana a matsayin hare-haren masu tsatsauran ra'ayi a ofisoshin 'yan sanda.

Zahedan shi ne yanki mafi talauci a Iran, da ke kan iyaka da Pakistan, kuma yana daya daga cikin garuruwan da Sunni ke da rinjaye a kasar, yayin da yake da yawan 'yan kabilar Baluch da ke da ra'ayin Sunni maimakon mabiya Shi'a a Iran.

Yankin dai ya kasance wurin da ake kai hare-hare kan jami'an tsaron kasar Iran da Tehran ta dora laifin a kan kungiyoyin 'yan sunni, yayin da kuma ake kallon yankin da ke kan iyaka a matsayin wata cibiyar safarar miyagun kwayoyi ta wasu kungiyoyi masu dauke da makamai.

Amnesty International ta ce a shekarar 2021 akalla kashi 19 cikin 100 na duk hukuncin kisa da aka aiwatar an yi ne kan 'yan kabilar Baluchi, wadanda ta ce sun kunshi kashi biyar cikin dari na al'ummar Iran.

Rikicin dai ya barke ne makonni biyu da fara zanga-zanga a fadin kasar Iran domin nuna rashin amincewa da mutuwar Mahsa Amini, wanda 'yan sanda suka kama shi.

A cewar Amnesty, an kashe mutane 82, yayin da 66 suka rasa rayukansu a ranar 30 ga watan Satumba kadai, ciki har da yara uku.

Jami’an tsaro sun dakile zanga-zangar ta hanyar zubar da jini," in ji wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta Iran (IHR).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.