Isa ga babban shafi

EU ta lafta takunkumai kan Iran saboda dakile masu zanga-zangar kin jinin Hijab

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da daukar matakin kakabawa Iran takunkumai, bisa zargin gwamnatin kasar da yin amfani da karfi fiye da kima wajen murkushe masu zanga-zangar kin jinin Hijabi wadda ta samo asali daga zargin kisan Mahsa Amini a hannun jami’an tsaro.

Masu zanga-zangar kin jinin Hijabi a Iran.
Masu zanga-zangar kin jinin Hijabi a Iran. AP
Talla

Wasu jami'an diflomasiyyar Tarayyar Turai hudu sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, a jiya Laraba aka cimma yarjejeniyar laftawa Iran takunkumai, kuma taron ministocin harkokin wajen kasashen EU da zai gudana a Luxembourg ranar litinin mai zuwa shi ne a tabbatar da takunkuman a hukumance.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan takunkuman da ake shirin kakabawa Iran, amma tuni kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Canada suka dauki matakin kakaba nasu takunkuman na daban kan bangarorin tsaron kasar.

Zanga-zangar adawa da kisan Mahsa Amini dai ta juye zuwa tarzoma a sassan Iran bayan da fitattu daga ciki da wajen kasar suka fara goyon bayan masu zanga-zangar inda dandazon mata ke ci gaba da cire hijabansu suna konawa don nuna takaicinsu da yadda 'yan sandan tabbatar da da'ar ke tilastawa mata sanya hijabi.

Jami'an tsaron tabbatar da da'ar dai sun nanata cewa basu da hannu a kisan matashiyar mai shekaru 22 wadda aka kama da laifin sanya suturar da ta sabawa dokokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.