Isa ga babban shafi

Gobara ta hallaka fursunoni hudu a gidan yarin Iran

Aƙalla fursunoni huɗu suka mutu a ƙasar Iran sakamakon wata gobara da ta tashi a gidan yarin Evin da ke birnin Teheran cikin dare, kamar yadda ma'aikatar shari'a ta bayyana, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin mahukunta kari kan zanga-zangar da aka kwashe wata guda anayi saboda mutuwar Mahsa Amini.

Gidan yarin Evin dake arewacin birnin Tehran, inda gobarar ta tashi a yammacin ranar Asabar 15 ga watan Oktoba.
Gidan yarin Evin dake arewacin birnin Tehran, inda gobarar ta tashi a yammacin ranar Asabar 15 ga watan Oktoba. AFP - -
Talla

Hukumomin Iran dai sun dora alhakin tashin gobarar a kan " tarzoma da fadace-fadace" da aka samu tsakanin fursunonin, sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ce ba zasuyi gaggawar amince wa da bayanan hukumomi ba.

Ma’aikatar shari’ar ta wallafa cewa "Fursinoni hudu ne suka mutu sakamakon shakar hayakin da gobarar ta haddasa, sannan wasu 61 suka jikkata.

Sanarwar tace wasu hudu na cikin “mawuyacin hali, amma anyi nasarar kashe gobarar.

'Yan uwa da kungiyoyin kare hakkin fursunonin sun bayyana tsananin fargaba, kuma sun ce hukumomi sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a gidan yari.

Karar harbe-harbe

An rika jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a lokacin gobarar daga cikin rukunin, da ke ci da wuta da hayaki, kamar yadda wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna.

Gobarar ta zo ne bayan zanga-zangar makwanni hudu da aka kwashe ana yi kan mutuwar Amini mai shekaru 22 da haihuwa, bayan kama ta da laifin keta ka'idojin sanya hijabi a Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.