Isa ga babban shafi

Najeriya: Fursunonin kusan kashi 70 ne ke jiran hukunci

Gwamnatin Najeriya tace kusan kashi 70 na mutanen dake garkame a gidajen yarin kasar, mutanen da ake zargi da aikata laifuffuka ne, amma kuma ba a kai ga yanke musu hukunci a gaban kotuna ba.

Masana shari'a na danganta cunkoson da ake samu a gidajen yari, da rashin yanke hukunci akan lokaci daga kotuna
Masana shari'a na danganta cunkoson da ake samu a gidajen yari, da rashin yanke hukunci akan lokaci daga kotuna © punch
Talla

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka, inda yake cewa yanzu haka daga cikin mutane dubu 75 da dari 635 dake gidajen yarin Najeriya, dubu 51 da dari 541 duk masu jiran alkalai su yankewa hukunci ne, abinda ya ke nuna cewar sune kashi 68.

Aregbesola yace matsalar na ciwa ma’aikatarsa tuwo a kwarya saboda makudan kudaden da ake kashewa a kansu da kuma ma’aikatan tsaron dake musu hidima wajen kula da su.

Ministan yace abin takaici shine wasu daga cikin wadanda ake tsare da su a gidajen yarin ma babu wata shaida a rubuce akan dalilin tsare su, saboda dadewar da sukayi a gidan yarin ya sa takardun su sun bata.

Aregbesola yace ana samun mutanen dake kwashe shekaru 10 zuwa 20 ba tare da an kammala shari’arsu ba, yayin da wasu kuma kan gurfana a gaban alkalai 5 zuwa 6 ba tare da an kammala shari’ar da ake musu ba.

Ministan yace dokar kasa ta basu umurnin aje wadannan mutane ne, kuma abinda suke yi kenan, yayin da yiwa irin wadannan mutane shari’a da kuma yanke musu hukunci ya rataya akan kotuna.

Masana harkar shari’a na danganta tsaikon da ake samu wajen rashin kammala shari’a da wuri daga 'yan sanda wajen rashin gabatar da kwararan shaidu, sai kuma alkalai dake jinkirin yanke hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.