Isa ga babban shafi

Yawan mutanen da ake zartas wa hukuncin kisa a Iran ya karu da kashi 75

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na IHR da ECPM sun ce mahukuntan Iran sun kara yawan mutanen da suke zartas wa da hukuncin kisa zuwa kashi 75 cikin 100 a shekarar 2022, matakin da masu kare hakkin na dan adam suka ce ana dauka domin tsorata masu zanga-zangar adawa da gwamnati.

Wani allo mallakin masu zanga-zangar adawa da gwanatin Iran bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini.
Wani allo mallakin masu zanga-zangar adawa da gwanatin Iran bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini. © REUTERS/Michele Tantussi
Talla

Alkalumman da aka fitar dai sun nuna cewar, mutane 582 aka zartas wa da hukuncin kisa ta hanyar rataya a Iran cikin shekarar da ta gabata, adadi mafi yawa tun shekarar 2015.

A 2022 zanga-zanga ta barke cikin watan Satumba a fadin Iran, sakamakon mutuwar Mahsa Amini, 'yar kabilar Kurdawa mai shekaru 22 da aka kama bisa zargin keta ka'idojin sanya tufafi ga mata.

Mahukuntan kasar dai sun mayar da martanin amfani da karfi wajen murkushe zanga-zangar tare da kama mutane da dama, lamarin da ya kai ga rataye wasu mutane hudu bayan shari’ar da aka yi musu akan boren da suka yi.

Daraktan kungiyar kare hakkin dan Adam ta IHR Mahmood Amiry Moghaddam ya ce a yayin da sa idon manyan hukumomi da kasashe ya hana mahukuntan Iran ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa kan wadanda suka samu da laifi  wajen tayar da hankali a zanga-zangar da aka yi a watannin baya, gwamnatin Iran ta ci gaba da aiwatar da hukuncin na kisa kan wasu tuhume-tuhume da take amfani da su wajen tsoratar da jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.