Isa ga babban shafi

Sama da mutum 400 aka kashe a zanga-zangar Iran - Bincike

Jami’an tsaron kasar Iran sun kashe akalla mutane 448 a wani samame da aka yi na murkushe zanga-zangar da ta fara a tsakiyar watan Satumba, kamar yadda wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta bayyana a ranar Talata.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Iran
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Iran AP - Francisco Seco
Talla

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Norway mai cibiya a Iran din ta bayyana cewa, daga cikin mutane 448 da aka tabbatar an kashe su, 60 yara ne 'yan kasa da shekaru 18, ciki har da 'yar mata tara, da mata 29.

Kungiyar ta ce jami’an tsaro sun kashe mutane 16 a cikin makon da ya gabata kadai, inda aka kashe 12 daga cikinsu a yankunan Kurdawa wato inda zanga-zangar ta fi karfi.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce adadin wadanda suka mutu a makonnin da suka gabata ya karu bayan an tantance. Adadin wadanda suka mutu ya hada da ‘yan kasar da aka kashe a harin da ba na jami’an tsaro ba.

Birgediya Janar Amirali Hajizadeh na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a ranar Talata ya ce sama da mutane 300 ne aka kashe, wanda shi ne karon farko da mahukuntan kasar suka amince da wannan adadi.

Zanga-zangar ta barke ne bayan mutuwar Mahsa Amini a ranar 16 ga watan Satumba wanda jami'an 'yan sanda kama abin da ya janyo kalubale mafi girma ga gwamnatin tun bayan juyin juya halin 1979.

Mafi yawan wadanda suka mutu sun kasance a yankin kudu maso gabashin Sistan-Baluchistan inda aka kashe mutane 128 bayan zanga-zangar da ta barke, in ji IHR.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.