Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kawo karshen rundunar MUNISMA a Mali
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da kawo karshen ayyukan rundunar sojin Majalisar a Mali wato Minusma, kamar dai yadda gwamnati Mali ta bukata.
Wallafawa ranar:
Kwamitin Tsaron ya kada kur’ar ne da gagarumin rinjaje domin kawo karshen ayyukan wannan runduna da aka kafa tun a shekara ta 2013, domin taimaka wa Mali ta yaki ayyukan ta’addanci da kuma wanzar da zaman lafiya a kasar.
An dai kada Kuri’ar ne makonni biyu bayan da ministan harkokin wajen kasar Abdoulaye Diop, ya gabatar da bukatar hakan a gaban Majalisar, inda ya zargin rundunar ta Minusma da nuna gazawa a cikin ayyukanta.
Karkashin wannan kuduri da aka amince da shi a yau jama’a, daga yau 30 ga watan Yuni rundunar ta kawo karshen ayyukanta, to sai dai ba kamar yadda Mali ta bukata na ganin an kammala aikin janye dakarun a cikin watanni uku ba, dakaru za su ci gaba da janyewa sannu a hankali har zuwa ranar 31 ga watan Disambar wannan shekara.
Lokacin da aka faramahawarardangane da wannan batu, kasashenFaransa da Amurkasunbukaci a bai wadakarunwatanni 18 domin janyewa, indadagakarshe aka amince da watanni 6 watoranar 31 ga watan Disambamaizuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu