Isa ga babban shafi

Makomar Mali bayan janye dakarun MINUSMA

A wannan Jumu’ar ce Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke zaman kada kuri’a game da yiwuwar tsawaita ko kuma janye dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar da ke aiki a kasar Mali.

Wasu daga cikin dakarun Minusma a Mali
Wasu daga cikin dakarun Minusma a Mali AFP - SIA KAMBOU
Talla

Wasu majiyoyin diflomasiya sun ce, a yayin da ake ganin watakila a kawo karshen ayyukan sojin wanzar da zaman lafiyar a Mali, yanzu haka ana fadi-tashi kan wata tattaunawa a Majalisar Dinkin Duniya game da tsara yadda za a kwashe dakarun a daidai lokacin da gwamnatin Bamako ke cewa, tana son a janye su cikin gaggawa.

A ranar 16 ga watan Yunin da ya gabata ne, Ministan Harkokin Wajen Mali, Abdoulaye Diop cikin wani yanayi na ban al’ajabi kuma a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya  ya  bukaci a gaggauta janye dakarun, yana mai caccakar gazawar rundunar ta Minusma.

Aikin wanzar da zaman lafiya na Minusma a Mali, shi ne mafi tsada da aka gudanar karkashin Majalisar Dinkin Duniya, domin kuwa yana lakume dala biliyan 1 da miliyan 200 a kowacce shekara.

Sai dai a yanzu, bisa dukkan alamu za a kawo karshen aikin rundunar ta Minusma a kasar ta Mali wadda ke fama da hare-haren ta’addanci, yayin da ake fargabar makomar wannan kasa.

A farkon watan Yuni ne, Sakatere Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana ci gaba da zaman Minusma a Mali a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci, abin da yasa ake ganin cewa, ayyukan ta’addanci za su fadada a yankin da zaran an janye rundunar.

Kodayake daya daga cikin muhimman ka’idojin aikin wanzar da zaman lafiya shi ne, samun izini daga gwamnatin kasa.

Wani kudiri da Faransa ta gabatar a ranar Laraba da ta gabata wanda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya gani, na nuni da cewa, Kwamitin Tsaron zai kawo karshen ayyukan rundunar ta Minusma a Mali karkashin wani kudirin doka mai lamba 2,640 wanda za a zartar a ranar 30 ga watan Yunin 2023, ma’ana a wannan Juma’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.