Isa ga babban shafi

Abin takaici ne yadda rayukan tarin fararen hula ke salwanta a yaki- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda mahukuntan kasashe ke gaza bayar da kariya ga fararen hular da basu jiba basu gani ba a lokacin rikici ta yadda ake samun karuwar mutuwar irin fararen hular a tashe-tashen hankulan da Duniya ta ke gani cikin shekarar nan da akalla karuwar kashi 53 idan an kwatanta da shekarun baya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterress.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterress. © REUTERS / ANDRONIKI CHRISTODOULOU
Talla

Sakataren Janar na majalisar Antonio Guterres ya ce gwamnatoci da saurann hukumomi sun gaza wajen kare rayuka da dukiyar miliyoyin fararen hular da tashe-tashen hankula ko yaki suka rutsa da su. 

A cewar Guterres idan aka kwatanta da alkaluman shekarar 2022 matsalar salwantar rayukan fararen hula ya karu da kashi 53 cikin 100, wanda ke da nasaba da sakacin mahukuntan kasashen da ke rikici ko kuma aka samu barkewar yaki.

Rahoton da Majalisar ta fitar ya nuna cewar fararen hula kusan dubu 17 suka mutu a cikin tashe-tashen hankula har kashi 12 da suka barke a shekarar da ta gabata cikin kasashe daban-daban, ciki har da yake-yaken kasashen Ukraine da Sudan da Habasha da kuma Syria, inda a nan ne matsalar tafi kamari. 

Guterres ya kara da cewa alkaluman da suka tattara na nuni da cewar kashi 94 cikin 100 na adadin wadanda hare-haren bam suka halaka cikin shekarar bara a yankuna masu cinkoson jama fararen hula ne. 

A kasar Ukraine kadai, wadda dakarunta ke gwabza yaki da takwarorinsu na Rasha yau sama da shekara guda, majalisar ta ce, fararen hula kusan dubu 8 ne suka mutu, yayin da wasu fiye da dubu 12 suka jikkata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.