Isa ga babban shafi

Hare-haren Rasha ta sama ya kashe fararen hula 16 a Ukraine

Hare-haren Rasha ta sama sun afkawa biranen Ukraine da safiyar Juma'a, inda aka samu asarar rayukan akalla mutane 19 daidai lokacin da gwamnatin Kyiv ta ce tana dab da kai farmakin da ake kyautata zaton za a kai kan dakarun Moscow.

Dakarun Ukraine suna musayar wuta da Masu kishin Rasha a Slaviansk.
Dakarun Ukraine suna musayar wuta da Masu kishin Rasha a Slaviansk. REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Hare-haren na gomman makamai masu linzami ya kawo karshen jinkirin da aka samu na makonni wanda Rasha ke ci gaba da kaiwa da nufin gurgunta tashar makamashin Ukraine a cikin watannin hunturu.

Wadannan munanan hare-haren sun hada da wani harin da aka kai a wani katafaren gida a Uman da ke tsakiyar kasar Ukraine, inda wakilin AFP yace yaga yadda masu aikin ceto, ke zakulo gawarwakin da suka makale a karkashin baraguzan gine-gine.

Masu aikin ceto na amfani da sanduna don nemo wadanda suka tsira daga cikin ragowar rukunin gidaje masu yawan hawa da ke tsakiyar birnin da mutane sama da 80,000 ke zaune.

Gwamnan yankin Igor Taburets ya ce wasu makamai masu linzami guda biyu sun sauka a birnin, inda suka kashe mutane 17 ciki har da yara biyu ‘yan shekaru 10.

Sabbin hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da ministan tsaron kasar Ukraine Oleksiy Reznikov ya ce shirye-shiryen da kasarsa ke yi na tunkarar matsugunan Rasha ya kusa kammaluwa.

Kungiyar tsaro ta NATO tare da kawayenta sun taimakawa Ukraine da motocin yaki 1,550 da kuma tankoki na yaki 230, domin taimaka mata wajen kwato yankunanta daga hannun dakarun Rasha, in ji shugaban kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.