Isa ga babban shafi

Rahoton MDD ya bankado yadda Sojin Mali suka kashe fararen hula 500

Wani rahoton majalisar Dinkin Duniya ya bankado yadda sojin Mali da taimakon sojojin ketare da ke aiki tare da su da sunan yaki da ta’addanci, suka kashe fararen hular da yawansu ya tasamma 500 a cikin watan Maris din shekarar 2022 da ta gabata.

Wasu sojojin Mali zagaye da Kanal Assimi Goïta da ke jagorancin gwamnatin Sojin kasar.
Wasu sojojin Mali zagaye da Kanal Assimi Goïta da ke jagorancin gwamnatin Sojin kasar. © AP
Talla

Rahoton wanda hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar a yau juma’a ya ce wannan kisan gilla shi ne mafi munin tashin hankali da Mali ta gani tun bayan ta’azzarar ayyukan ta’addanci a sassan kasar cikin shekarar 2012.

Majalisar ta bayyana cewa wannan shi ne kunshin bayanai mafi muni kan aika-aikar da Sojojin na Mali da taimakon sojin ketare ke yi wa jama’ar kasar ta hanyar azabtarwa da kisan gilla kan wadanda basu ji ba basu gani ba.

Duk da cewa rahoton na Majalisar Dinkin Duniyar bai fito karara ya bayyana sunan kasar da Sojojin ketaren a Mali suka fito ba, amma yanzu haka Sojin hayar kamfanin tsaro na Wagner mallakin Rasha ne kadai ke taimakawa gwamnatin Sojin kasar da sunan yaki da ayyukan ta’addanci.

Rahoton ya ce wannan kashe kashe ya faru ne a tsakanin ranaku 27 zuwa 30 ga watan Maris din shekarar ta 2022 inda sojojin hayar da na Mali suka kashe fararen hular da yawansu ya kai 500 a garin Moura, lamarin da rahoton ke cewa ya yi karantsaye ga dokokin kasa kasa dama dokokin kare hakkin dan adam.

Rahoton wanda aka jima ana dakon fitarsa, kwararrun hukumar kare hakkin dan adam da ke cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar dinkin duniya a Mali sun shafe tsawon lokaci suna gudanar da bincike a yankin da kashe-kashen ya faru gabanin tattara alkaluma.

A cewar rahoton akwai akalla mata 20 da kananan yara 7 wadanda ke cikin mutanen da sojojin suka yi wa kisan gilla yayinda wasu mata 58 ciki har da masu karanciin shekaru suka fuskanci cin zarafi ta hanyar fyade a yankin.

Rahoton ya bayyana cewa akwai kuma tarin mutane da suka fuskanci matsananciyar azabtarwa daga sojojin bayan kame su tare da daure su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.