Isa ga babban shafi

Sojojin Majalisar Dinkin Duniya 7 sun jikkata a Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarunta na wanzar da zaman lafiya 7 ne suka samu raunuka a tsakiyar kasar Mali ranar Asabar bayan da wani bam da aka dana a gefen hanya ya tashi a karkashin ayarin motocinsu.

Dakarun Minusma a yankin Tombouctou na kasar Mali, 08/12/21.
Dakarun Minusma a yankin Tombouctou na kasar Mali, 08/12/21. © FLORENT VERGNES/AFP
Talla

Cikin sanarwa da rundunar MINUSMA ta fitar ta shafukan sada zumunta yanzu haka sojojin na samun kulawa a wani asibiti ba tare da karin bayani kan yanayin da suke ciki ba ko kasar da suka fito.

Bam din ya tashi ne a lokacin da ayarin motocin ke kan hayarsa ta zuwa kauyn Douentza dake arewacin kasar.

Rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kai makamaita hare-hare kan dakarunta har sau shida a cikin wannan shekara a tsakiyar Mail, dake fama da kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.