Isa ga babban shafi

Dubban 'yan Mali sun gudanar da zanga-zangar kin jinin dakarun MDD

Dubban ‘yan kasar Mali sun gudanar da zanga-zangar kin jinin ci gabana da zaman dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar, yayinda da dama daga cikin masu zanga-zangar a tsakar birnin Bamako suka rike tutar Rasha a gangamin.

Masu zanga-zangar kin jinin Dakarun Majalisar Dinkin Duniya.
Masu zanga-zangar kin jinin Dakarun Majalisar Dinkin Duniya. AP - Harandane Dicko
Talla

Alaka tsakanin gwamnatin Sojin Mali da dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke wanzar da zaman lafiya a kasar MINUSMA ta kara tsami ne tun cikin watan Yulin da ya gabata, bayan da gwamnatin ta kame Sojin Ivory Coast da ta zarga da kasancewa Sojojin haya.

Dubban masu zanga-zangar rike da kwalayen da ke dauke da rubutun bama bukatar MINUSMA a kasarmu, sun ce suna bukatar ficewar dakarun domin basu taimakawa kasar da komi.

Guda cikin masu zanga-zangar Lassina Doumbia ta bayyana cewa suna kaunar kasarsu kuma suna kaunar Sojojin da ke mulki karkashin Kanal Assimi Goita.

Wani matashi na daban Samba Wangara a cikin masu zanga-zangar ya ce  basa bukatar taimakon majalisar dinkin Duniya, shugaban mu ya wadatar mana.

Masu zanga-zangar sun zargin rundunar ta MINUSMA da zagon kasa ga gwamnatin Sojin Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.