Isa ga babban shafi

Mali ta kame sojojin Faransa biyu kafin daga bisani ta salleme su

Mahukunta a Mali sun cafke jami’an sojin Faransa biyu ranar alhamis a birnin Bamako bisa zargin leken asiri, kafin daga bisani a sallame su safiyar wannan juma’a

Sojojin rundunar Barkhane ta Faransa, 7 ga watan maris 2016.
Sojojin rundunar Barkhane ta Faransa, 7 ga watan maris 2016. PASCAL GUYOT / AFP
Talla

Majiyar diflomasiyyar Faransa ta ce, jami’an sojin biyu an kama su ne daidai lokacin da suke daukar hotuna a cikin birnin Bamako, hotunan da majiyar ke cewa suna dauka don tsara yadda za a iya kwashe Faransawa daga birnin idan bukatar hakan ta taso.

Tun a marecen ranar alhamis ne aka fara yada bayanan da ke cewa «an kama jami’an leken asirin Faransa biyu daidai lokacin da suke daukar hotuna a wasu muhimman wurare na barikin soji a birnin Bamako.»

Ana kara samun fargabar shiga zaman tankiya tsakanin mahukuntan Paris da takwarorinsu na Bamako, yayin da bayanai ke cewa ofishin jakadancin Faransa ya kasance a rufe safiyar wannan juma’a a Bamako, kafin daga bisani a sake bude shi.

Kokarin da Radio France Internationale ya yi don jin martanin ma’aikatar tsaro ko ta harkokin wajen kasar Mali dangane da wannan lamari ya ci tura, saboda ba wanda ke son yin tsokaci a kai.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da alaka ke kara yin tsami tsakanin kasashen biyu, musamman daga lokacin da Mali ta kori jakadan Faransa daga birnin Bamako da kuma janyewar dakarun Barkhane daga cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.