Isa ga babban shafi

Fararen hula na zanga-zangar goyon bayan Sojoji a Sudan

Tarin fararen hula ‘yan kabilar Beja ne suka tsunduma zanga-zangar nuna goyon baya ga sojoji a Sudan yau laraba dai dai lokacin da yaki ke ci gaba da tsananta bayan mutane fiye da dubu 700 daga matsugunansu.

Wasu 'yan Sudan da ke zanga-zanga.
Wasu 'yan Sudan da ke zanga-zanga. AFP - EBRAHIM HAMID
Talla

‘Yan kabilar ta Beta wadanda suka yi dafifi a tsakar garin na su mai tazarar kilomita 850 daga birnin Khartoum ta bangaren gabar ruwa, sun rika daga kwalaye dauke da rubuce-rubucen bukatar basu damar yaki don taimakon sojoji.

Mahmoud al-Bichari guda cikin masu zanga-zangar ya shaidawa manema labarai cewa a shirye su ke su fita yaki don taimakawa Sojoji da nufin dawo da zaman lafiya kasar.

Cikin kwanaki 25 da faro yakin na Sudan har zuwa yanzu an gaza shawo kan bangarori biyu da ke yaki da juna musamman bayan rushewar tattaunawar sulhun da ta gudana a birnin Jedda wadda Saudiya da Amurka ke jagoranta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu alamun iya kawo karshen rikicin kwana kusa lura da yadda aka haura makwanni 3 ana yakin na Sudan ba tare da sararawa ba.

A ranar 15 ga watan Aprilu ne rikicin ya barke tsakanin jagoran mulkin Sojan Sudan Abdel Fattah al-Burhane da Janar Mohamed Hamdane Daglo shugaban dakarun soji na RSF, dakaru biyu da suka hada hannu wajen jagorantar juyin mulkin watan Oktoban 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.