Isa ga babban shafi

Bakin haure 440 aka kubutar daga gabar ruwan Italiya

Kungiyar agaji ta Doctors Without Borders ta ce an kubutar da bakin haure 440 daga gabar tekun Malta, bayan wani aikin ceto da jami’an agaji suka dauki tsawon sa’o’I goma sha daya suna gudanar wa a yankin mai cike da hatsari.

Wasu bakin Haure cikin karamin kwale kwale da aka ceto daga teku.
Wasu bakin Haure cikin karamin kwale kwale da aka ceto daga teku. © GONZALO FUENTES / REUTERS
Talla

MSF ta ce jirgin ruwanta na Geo Barents ya yi aiki tukuru a cikin dare, wajen ceton saboda tsananin yanayin sanyi, bayan an yi amfani da rigar kariya, wajen kare su daga nutsewa a ruwa.

Kungiyar a shafinta na Twitter ta bayyana cewa, kimanin mutane 440, ciki har da mata 8 da yara 30, aka ceto, kuma yanzu haka suna cikin koshin lafiya.

Italiya na fuskantar karuwar masu yin kaura daga arewacin Afirka, inda bakin haure sama da 28,000 suka shiga kasar tun daga farkon shekarar nan zuwa yanzu.

Kakakin kungiyar Flavia Pergola ta ce, 'yan ci-ranin da MSF ta ceto sun shafe kwanaki hudu a cikin teku, ba tare da abinci ko ruwa ba, bayan sun tashi daga gabashin Libya, kusa da Benghazi, a ranar 1 ga Afrilu.

Bakin hauren dai sun fito ne daga kasashen Syria da Pakistan da Bangladesh da Masar da Somalia da kuma Sri Lanka inda yanzu haka za a mika su kasar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.