Isa ga babban shafi

Sama da bakin haure 1,000 ne aka sauke a tashoshin ruwan Italiya

Sama da bakin haure 1,000 ne aka ceto a wasu tashoshin jiragen ruwa biyu na Italiya bayan cunkoson kwale-kwalen da suke ciki saman tekun Bahar Rum, kamar yadda masu gadin gabar tekun suka sanar.

 Jirgin ceton bakin haure
Jirgin ceton bakin haure Handout / ITALIAN POLICE / AFP
Talla

An yi nasarar ceton ne a daidai lokacin da aka gano gawar mutum na 74 da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su kusan makonni biyu da suka gabata,gawar na wata yarinya 'yar shekara biyar zuwa shida, a cewar kamfanin dillancin labarai na AGI.

Hatsarin jirgin na ranar 26 ga watan Fabrairu, wanda ya afku a kusa da gabar tekun Calabria, ya janyo kakkausar suka ga gwamnatin hannun dama karkashin jagorancin Firaminista Giorgia Meloni, kan gazawarta wajen shiga tsakani a kan lokaci domin ceto jirgin dake dauke da bakin haure..

Wani jirgin ceton bakin haure a yankin Lampedusa
Wani jirgin ceton bakin haure a yankin Lampedusa © Mauro Buccarello/AP

Jami'an tsaron gabar tekun sun ce a yau asabar sun kawo karshen wani aikin ceto da aka fara a ranar Juma'a bayan da aka hangi jiragen ruwa guda uku suna bi ta gabar tekun Italiya.

Hotunan masu gadin bakin teku sun nuna wani katon jirgin ruwan kamun kifi cikin aiki a kokarinsa na ceto mutanen.

Wadannan bakin haure 487 da ke cikin kwale-kwalen na farko an kawo su tashar jiragen ruwa ta Crotone cikin koshin lafiya in ji masu gadin gabar tekun.

Jirgin na uku dauke da mutane 379 ya samu ceto daga wasu jiragen ruwa biyu masu aikin sintiri a gabar teku tare da mika bakin hauren zuwa wani jirgin ruwan sojojin ruwa da ya nufi tashar ruwan Sicilian na Augusta.

Ma'aikatar tsaron Italiya ta ce ta fara jigilar 'yan ci-rani daga cibiyar cunkoson bakin haure a tsibirin Lampedusa, wanda ta ce yanzu ya wuce gona da iri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.