Isa ga babban shafi

Amurka ta yi mana rashin adalci - Habasha

Gwamnatin Habasha ta zargi Amurka da rashin adalci saboda yadda ta dora mata laifukan yakin da aka aikata na tsawon shekaru biyu a rikicin yankin Tigray.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken. © AFP - PETR DAVID JOSEK
Talla

Ma’aikatar Harkokin Wajen Habasha ta bayyana cewa, zargin na Amurka ya dauki bangaranci kuma sanarwar da ta fitar ta tunzuri ce kawai.

A ranar Litinin ne Washington ta zargi daukacin bangarorin da suka fafata a rikcin na Tigray da aikata laifukan yaki.

Sai dai Amurkar ta ware Habasaha da Eritrea da kuma dakarun Amhara, inda ta ce sun ci zarafin bil’adama a yayin yakin ba tare da ta ambaci ‘yan tawayen Tigray ba a wannan batu.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken wanda ya kai ziyararsa ta farko zuwa Habasha a makon jiya tun bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Habasha da ‘yan tawayen Tigray, ya  yi kakkarfan kira jim kadan da komawarsa Washington don ganin an gudanar da bincike.

A cewarsa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi kyakkawan nazarin dokoki da hujjoji, inda a karshe ta fahimci cewa, sojojin gwamnatocin Habasha da Eritrea da kuma ‘yan tawayen Tigray har ma da dakarun Amhara duk sun aikata laifukan yaki.

Sai dai Amurkar ba ta sanya sunan ‘yan tawayen Tigray ba a bangaren laifukan da ta ce, an aikata su da gan-gan kamar kisa da cin zarafin mata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.