Isa ga babban shafi

An aikata laifukan yaki a kasashen Habasha da Eritriya - Amurka

Amurka ta ce sojojin Habasha da Eritriya da kuma 'yan tawaye sun aikata laifukan yaki a lokacin kazamin rikicin da aka dauki tsawon shekaru biyu ana yi, kamar yadda sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana, kwanaki bayan ya ziyarci Addis Ababa.

Dakarun gwamnatin Habasha lokacin da suke kokarin shiga garin Mekele, da ke yankin Tigray a Arewacin kasar. An dauki wannan hoto a watan Mayun 2021.
Dakarun gwamnatin Habasha lokacin da suke kokarin shiga garin Mekele, da ke yankin Tigray a Arewacin kasar. An dauki wannan hoto a watan Mayun 2021. © Ben Curtis/AP
Talla

Blinken, wanda ya kai ziyara Habasha game da fatan samun zaman lafiya bayan cimma yarjejeniya a ranar 2 ga Nuwamba, ya yi kira da a dauki mataki kan wadanda suka ci zarafin bil’adama.

"Yawancin wadannan ayyukan da aka aikata ba sanadin yaki bane, da gangan aka yi su," in ji babban jami'in diflomasiyyar Amurka yayin da yake gabatar da rahoton kare hakkin bil'adama na Amurka na shekara-shekara.

Blinken ya kara da cewa ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta kuma gano "laifi na cin zarafin bil'adama" da sojojin Habasha, Eritriya da kuma Amhara, suka aikata, kodayake bai ambaci kungiyar Tigray ta ‘yan tawaye ba.

"Muna kira ga gwamnatin Habasha da gwamnatin Eritriya da kuma kungiyar TPLF da su dauki alhakin wannan ta'asa," in ji Blinken.

"Rikicin da aka yi a arewacin Habasha ya yi muni sosai. An kashe maza da mata da yara. An ci zarafin mata da 'yan mata. An tilastawa dubban mutane gudun hijira daga gidajensu. An kai wa daukacin al'ummomin hari musamman saboda kabilarsu," in ji Blinken.

Blinken ya kuma jawabi kan abubuwan da ya gudanar a lokacin tafiyarsa zuwa Addis Ababa, inda ya yi wata doguwar ganawa da Abiy Ahmed, sannan ya gana da babban shugaban kungiyar ‘yan tawayen Tigray Getachew Reda.

A baya dai Amurka ta yi kiyasin cewa kimanin mutane 500,000 ne suka mutu a rikicin na tsawon shekaru biyu, wanda ya sa ya kasance daya daga cikin yake-yake mafi muni a karni na 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.