Isa ga babban shafi

Abiy Ahmed ya yi ganawar farko da shugabannin yankin Tigray

Firaministan Habasha Abiy Ahmed a yau Juma'a ya yi ganawarsa ta farko ido da ido da shugabannin yankin Tigray tun bayan da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a bara, kamar yadda jami'ai da kafofin yada labaran kasar suka bayyana.

Zaman tattaunawa tsakanin Gwamnatin Habasha da yan tawayen Tigray
Zaman tattaunawa tsakanin Gwamnatin Habasha da yan tawayen Tigray AP - Themba Hadebe
Talla

Wannan tattaunawar na zuwa ne kusan watanni uku kenan tun bayan da gwamnatin Habasha da kuma kungiyar 'yan tawayen kabilar Tigray (TPLF) suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta bayan shafe shekaru biyu ana gwabza  yaki.

Mai baiwa Firaministan Habasha shawara kan harkokin tsaro Redwan Hussein ya fada a shafinsa na twitter cewa Abiy Ahmed da sauran jami'ai sun gana da tawagar kungiyar ta TPLF "dangane da ci gaban shirin zaman lafiya".

"Saboda haka, Firaminista Abiy ya yanke shawara game da kara yawan zirga-zirgar jiragen sama, banki da sauran batutuwan da za su karfafa amincewa da saukaka rayuwar fararen hula.

Kafofin yada labaran gwamnati sun ce wannan ne karon farko da Abiy ya shiga cikin abin da ake kira kwamitin daidaita aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kafa bayan yarjejeniyar da aka cimma a ranar 2 ga watan Nuwamba a Pretoria babban birnin  kasar Afirka ta Kudu.

Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin firaministan kasar Habasha kuma ministan harakokin wajen kasar Demeke Mekonnen da babban hafsan sojin kasar Birhanu Jula, tare da babban kwamandan sojan kabilar Tigray Tsadkan Gebretensae da kakakin kungiyar ta TPLF Getachew Reda, kamar yadda hotunan kafofin yada labaran kasar suka nuna.

Getachew ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta kasar Habasha, inda ya ce tattaunawar ta shafi bude harakokin banki da safarar filaye zuwa yankin Tigray.

A halin da ake ciki, gwamnatin kasar Habasha ta shiga wani farmakin diflomasiyya na neman goyon bayan yunkurinta na dakatar da ayyukan kungiyar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da ke da alhakin binciken hakkin bil adama a kasar.

Karamin ministan harakokin wajen kasar Mesganu Arga ya tattauna da jakadu daga Amurka da Birtaniya da dai sauransu, domin ganin an kawo karshen wa'adin kwamitin da ya kira na'urar nuna bangaranci a siyasance, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.