Isa ga babban shafi

Kasashen Duniya sun yi maraba da tsagaita wutar Habasha da 'yan tawayen Tigray

Kasashen Duniya sun yi maraba da matakin gwamnatin Habasha na kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ‘yan tawayen Tigray bayan shiga tsakanin kungiyar Tarayyar Afrika a wani taron sulhu na kwanaki 4 da ya gudana a Afrika ta kudu.

Zaman yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Habasha da wakilcin 'yan tawayen Tigray da ya gudana a Afrika ta kudu bisa jagorancin kungiyar Tarayyar Afrika.
Zaman yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Habasha da wakilcin 'yan tawayen Tigray da ya gudana a Afrika ta kudu bisa jagorancin kungiyar Tarayyar Afrika. © Siphiwe Sibeko/Reuters
Talla

Majalisar dinkin duniya ta bakin babban magatakardanta, Antonio Guterres ta jinjina wa wannan ci gaba da aka samu, tana mai bayyana shi a matsayin matakin farko na kawo karshen yakin, inda ta ce zai kawo sauki ga miliyoyin al’ummar Habasha fararen hula da suka tagayyara.

A yayin da ya ke bayyana ra’ayin gwamnatin kasar sa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya jinjina wa abin da ya kira namijin kokarin da masu shiga tsakani na Tarayyar Afrika suka yi wajen cimma wannan masalaha.

Shugaban Tarayyar Afrika, kuma shugaban Senegal Macky Sall, ya ce labarin tsagaita wutan yan a da matukar armashi, inda ya taya bangarorin da suka kai ruwa rana murna da suka dauko hanyar zaman lafiya na dindindin.

Shugaban Kenyan, wadda ke makwaftaka da Habasha, William Ruto ya jinjina wa Firaminista Abiy Ahmed da kuma shugabannin kungiyar ‘yan tawayen Tigray kan wannan matsaya da suka cimma na tabbatar da zaman lafiya.

Tarayyar Turai da Jamus sun mika sakon taya murnar su ga bangarorin biyu, suna masu cewa abin da ya rage yanzu shine maido da ayyukan jinkai a dukkan yankunan da yakin ya daidaita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.