Isa ga babban shafi

AU za ta jagoranci tattaunawa tsakanin Habasha da 'yan tawayen Tigray

Kungiyar kasashen Afirka AU ta sanar da sabuwar ranar da za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a kasar Habasha, taron da Afirka ta Kudu, za ta karbi bakunci.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed. AP - Mulugeta Ayene
Talla

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mashawarcin firaministan Habasha kan harkokin tsaro, Redwan Hussien, ya ce za a yi zaman sulhun ne tsakaninsa da ‘yan tawayen TPLF a ranar 24 ga watan Oktoba.

Tun da farko dai an shirya gudanar da tattaunawar ce a farkon wannan wata amma hakan ya faskara duk da yadda banagrorin biyu suka amince da shiga tattaunawa ko da ya ke gwamnatin karkashin jagorancin Abiy Ahmed ta ce fara tattaunawar bazai hana ta ci gaba da kakkabe barazanar tsaron da yankin na Tigray ke fuskanta ba.

Har zuwa yanzu dai mayakan kungiyar 'yan tawayen ta TPLF ba ta ce komai kan sauyin lokacin ba, amma a baya sun yi maraba da tattaunawar sulhu da gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.