Isa ga babban shafi

Habasha: Sojoji sun kwace ikon wasu yankuna da ke hannun 'yan Tigray

Dakarun kasar Habasha sun kwace garuruwa uku a yankin arewacin kasar, daya a arewa maso yamma, biyu kuma a kudancin babban birnin yankin Mekelle, kamar yadda fadar gwamnatin kasar ta ce ana kokarin kawo karshen rikicin.

Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021.
Wasu sojojin kasar Habasha yayin atasaye a yankin Amhara, ranar 14 ga Satumban shekarar 2021. © Amanuel Sileshi AFP/File
Talla

Sojojin Habasha da kawayenta da suka hada da na makwabciyarta Eritrea sun shafe shekaru biyu suna gwabzawa da sojojin Tigray, rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, da raba miliyoyi da muhallansu, ya kuma bar dubbai cikin matsananciyar yunwa.

Mai magana da yawun sojojin na Tigray bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba a cewar AFP. Tun da farko dai hukumomin yankin na Tigray sun amince da cewa sun rasa iko da shire.

Shire yana da nisan kilomita 140 daga arewa maso yammacin Mekelle, garin da ke da filin jirgin sama kuma yana daya daga cikin manyan garuruwan yankin. Ta dauki nauyin dubun dubatar mutanen da rikicin ya raba da muhallansu daga wasu yankuna.

Rikicin dai ya shafi Korem mai tazarar kilomita 170 da Alamata da ke da tazarar kilomita 180 kudu da Mekelle da kuma babban titin da ya nufi yankin da ke makwabtaka da yankin Amhara.

Wani mazaunin Mekelle ya ce mutane na ta yin tururuwar tara kayyakin amfanin yau da kullum, saboda fargabar da ake na cewa dakarun gwamnati da na Eritriya na iya isa wurin. Haka zalika, farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi da kashi 10% kuma ana sa ran zai kara tashi idan har sojoji suka yada zango a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.