Isa ga babban shafi

Lokaci na kurewa hukumomi wajen dakile kisan kiyashi a yankin Tigray- Tedros

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadin cewa, lokaci na kurewa ga hukumomi don hana kisan kiyashi a yankin Tigray na Habasha da ke fama da yakin basasa.

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Salvatore Di Nolfi
Talla

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaidawa manema labarai cewa, Duniya ba ta mai da hankali kan abinda ke faruwa a Tigray, lamarin da ka iya rikidewa zuwa kisan kare dangi.

Shugaban na WHO wanda dan asalin yankin na Tigray ne, ya jima yana kiraye-kiraye ga hukumomi da manya-manyan kasashe wajen ganin sun dauki matakan da suka kamata a kokarin dakile yakin na Habasaha.

Dai dai lokacin da yakin tsakanin 'yan tawayen yankin Tigray da kuma dakarun gwamnatin Habasha ke shirin cika shekaru 2 da fara, ko a talatar makon nan sai da Sojoji suka kwace wasu garuruwa 3 da ke hannun mayakan ta TPLF.

Matakin Sojin game da kwashe garuruwan na zuwa duk da yunkurin sasantawa don kawo karshen yakin wanda mabanbantan kungiyoyi ke shiga tsakani ciki har da kungiyar Tarayyar Afrika.

Gwamnatin Habasha ta ce a shirye ta ke ta amince da shiga tattaunawar zaman lafiya da 'yan tawayen sai dai hakan bazai hana ta ci gaba da kakkabe barazanar tsaron da ke yankin na Tigray ba.

Rikicin dai ya fara ne a ranar 4 ga Nuwamban shekarar, 2020, lokacin da Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya aike da sojoji zuwa yankin na Tigray bayan ya zargi jam'iyyar TPLF mai mulkin yankin da kai hari kan sansanonin sojojin tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.