Isa ga babban shafi

Gwamnatin Habasha ta sha alwashin karbe ikon yankin Tigray

Gwamnatin kasar Habasha ta lashi takobin karbe ikon filayen jiragen sama da wasu wurare dake yankin Tigray, yayin da a lokaci guda kuma ta nanata kudurinta na yin shawarwarin zaman lafiya.

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed AP - Mulugeta Ayene
Talla

Wannan ya zo ne daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da nuna damuwa kan rikici a yankin da yaki ya daidaita.

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba, yayin da fada ke kara kamari a arewacin Habasha.

Dakarun da ke goyon bayan gwamnati da na 'yan tawaye daga yankin Tigray suka shafe kusan shekaru biyu suna yaki da juna, abin da ya yi sanadiyyar rayuka da dama, inda dubbai suka tsere daga muhallansu.

Yankin Tigray mai dauke da mutane miliyan shida an mayar da shi saniyar ware, yayin da aka hanawa al’ummar yankin ababen more rayuwa kama daga lantarki, man fetur, abinci da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.