Isa ga babban shafi

An fara taron sulhunta rikicin Habasha a Afirka ta Kudu

Wakilan gwamnatin Habasha da dakarun Tigray da ke adawa da juna sun fara tattaunawar zaman lafiya a Pretoria, kamar yadda gwamnatin Afirka ta Kudu ta sanar, wanda ke zaman taro na farko a hukumance tsakanin bangarorin biyu da ke fada da juna bayan shafe kusan shekaru biyu ana kazamin rikici.

Gwamnatin Habasha ta fada a makon da ya gabata cewa dakarunta na mutunta hakkin dan adam.
Gwamnatin Habasha ta fada a makon da ya gabata cewa dakarunta na mutunta hakkin dan adam. © ABC
Talla

"Tattaunawar zaman lafiya, wadda aka kira domin samar da zaman lafiya da warware rikicin da ya barke a yankin Tigray, an fara shi ne a yau, 25 ga watan Oktoba, kuma za a kawo karshen tattaunawar ranar 30 ga watan," in ji Vincent Magwenya, kakakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa.

Magwenya ya ce Afirka ta Kudu a shirye ta ke ta zama mai masaukin baki da kuma ba da taimako ga tattaunawar zaman lafiya, inda ya kara da cewa, kasar na fatan tattaunawar za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa ga al'ummar Habasha.

Tawagar kungiyar Tarayyar Afirka karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ne ke shiga tsakani, tare da tsohon shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Phumzile Mlambo-Ngcuka.

Rikicin dai ya faro ne a watan Nuwamban shekarar 2020 lokacin da Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya aika da sojoji zuwa yankin Tigray, bayan harin da aka kai sansanonin soji. Tun daga wannan lokacin, rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ya kuma raba miliyoyi da muhallansu, tare da barin dubun-dubatar mutane cikin halin yunwa.

Tattaunawar, wacce aka jinkirta a farkon wannan watan saboda wasu dalilai, ta samu kwarin gwiwa daga Amurka. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, fadar White House ta ce ta kuduri aniyar ci gaba da shiga tsakani a kokarin samar da zaman lafiya a yankin na Tigray mai fama da rikici, sannan ta kuma ce ta damu matuka kan rahotannin tashin bama-bamai da kashe-kashe da ake samu.

Fara tattaunawar ya biyo bayan karuwar fadace-fadace tun bayan da aka karya yarjejeniyar jin kai a watan Agusta. A makon da ya gabata ne sojojin Habasha suka karbe iko da garuruwa uku wato Shire, Alamata da kuma Korem daga hannun ‘yan tawaye a yankin Tigray, lamarin da ya haifar da fargabar cewa sojojin za su ci zarafin fararen hula.

Wani bincike na hadin gwiwa a shekarar da ta gabata da Majalisar Dinkin Duniya da hukumar kare hakkin bil adama ta kasar Habasha suka fitar, ya nuna cewa dukkan bangarorin da ke yaki da juna, sun aikata laifukan da ka iya kaiwa ga laifukan yaki.

Gwamnatin Habasha ta fada a makon da ya gabata cewa dakarunta na mutunta hakkin dan adam.

Kwamishinan kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk, ya yi gargadin a makon da ya gabata cewa, hare-haren sama a yankin da ake fama da rikici na da matukar hadari a kan fararen hula, kwana guda bayan da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa yakin yana kara kamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.