Isa ga babban shafi

Tawagar jami'an gwamnatin Habasha za ta ziyarci Tigray

Tawagar jami’an gwamnatin kasar Habasha sun kama hanyar zuwa yankin Tigray da ke arewacin kasar, domin sa idanu akan shirin aiwatar da kudurorin yarjejeniyar zaman lafiyar, da aka kulla tsakanin ‘yan tawayen TPLF da gwamnati a cikin watan da ya gabata.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed da kakakin majalisar dokokin kasar Tagesse Chafo
Firaministan Habasha Abiy Ahmed da kakakin majalisar dokokin kasar Tagesse Chafo © REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo
Talla

Karo na farko kenan cikin shekaru biyu da manyan jami’an gwamnatin Habasha suka ziyarci yankin Tigray, wanda kazamin yaki ya tagayyara.

A ranar 2 da kuma 12 ga watan Nuwamban da ya gabata, mayakan TPLF suka amince da kulla yarjejeniyar ajiye makamansu, bayan shafe shekaru biyu suna fafatawa da sojojin gwamnati, tare da baiwa jami’an ayyukan jin kai damar shiga yankin Tigray don talllafawa miliyoyin mutanen da yunwa ta galabaitar.

Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu, wasu miliyoyi kuma suka rasa muhallansu, a rikicin na Tigray da ya shafi wasu yankunan Amhara da Afar da ke Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.