Isa ga babban shafi

Binciken MDD kan Tigray ka iya wargaza shirin zaman lafiya - Habasha

Kassar Habasha ta yi gargadin cewa kokarin da masu bincike da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya kan cin zarafin da aka yi a yakin arewacin kasar na iya kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a bara.

Tawagar da ta jagorancin shirin yarjejeniyar zaman lafiyar Habasha a Afirka ta Kudu
Tawagar da ta jagorancin shirin yarjejeniyar zaman lafiyar Habasha a Afirka ta Kudu AP - Themba Hadebe
Talla

A cikin watan Nuwamba ne gwamnatin Habassha da kungiyar ‘yan kabilar Tigrai  suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Afrika ta Kudu, domin kawo karshen yakin na yankin Tigray wanda aka debi tsawon shekaru biyu ana gwabzawa, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da haifar da matsalar jin kai a kasar da ke nahiyar Afirka.

A cikin rahotonta na farko da aka wallafa a watan Satumban bara, hukumar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa kan kasar Habasha mai samun goyon bayan MDD, ta ce ta samu shaidu kan keta haddi daga dukkan bangarorin biyu da hakan ka iya kaiwa ga laifukan yaki da cin zarafin bil adama.

Gwamnatin Habasha ta yi watsi da rahoton tare da fara amfani da tsarin diflomasiyya don samun goyon bayan kasashen duniya kan yunkurinta na dakatar da hukumar daga ci gaba da ayyukanta.

A ranar Laraba, mataimakin firaministan kasar Habasha, kuma ministan harkokin wajen kasar, Demeke Mekonnen, ya bayyana cewa, hukumar za ta iya gurgunta shirin samar da zaman lafiya karkashin jagorancin kungiyar AU, da shirin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya na Pretoria, da kalamai masu tayar da hankali, yana mai nuni da kungiyar tarayyar Afrika, wadda ta shiga tsakani a shawarwarin.

Kwamitin mai mambobi uku, wanda hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, ya bukaci gwamnatin Habasha, kawayenta Eritriya da kuma kungiyar ta ‘yan Tigray da su gudanar da bincike tare da gurfanar da duk masu aikata laifuka a gaban kuliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.