Isa ga babban shafi

Kasashe sun fara kai dauki ga Turkiya da Syria bayan kakkarfar girgizar kasa

Manyan kasashe sun fara taimakawa Turkiya da Syria wadanda suka wayi gari da mummunan ibtila’in girgizar kasa mai karfin maki 7.8 wadda zuwa yanzu ta kashe mutane fiye da dubu 2.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 zuwa yanzu ta kashe mutanen da suka haura 200 a kasashen biyu.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 zuwa yanzu ta kashe mutanen da suka haura 200 a kasashen biyu. AP
Talla

Girgizar kasar wadda shugaba Recep Tayyib Erdogan ya bayyana da mafi muni da Turkiyya ta gani tun shekarar 1939 tuni manyan kasashe ciki har da kungiyar Tarayyar Turai suka fara aikewa da jami’an agaji na musamman inda kwamishinan da ke sa ido kan rikice rikice na EU Janez Lenarcic ke cewa tawagar jami’ai na musamman daga kasashen Netherlands da Romania sun isa Turkiya.

Ita ma Faransa ta bakin shugaba Emmanuel Macron da ke jajantawa al’ummar kasashen na Turkiya da Syria ya ce a shirye suke su bai wa kasashen agaji, yayinda Rishi Sunak na Birtaniya ke cewa za su yi dukkan abin da za su iya wajen taimakon kasashen biyu.

Shi ma shugaba Vladimir Putin na Rasha wanda tuni jami’ansa suka isa kasashen biyu, ya mika da sakon jaje ga Syrian da turkiya yayinda Volodymyr Zelensky ke cewa za su taimakawa kasar don fita daga matsalar.

Sauran kasashen da jami’an agajinsu ke kan hanya don taimakon Turkiyan da Syria sun kunshi Spain da Iran da India da Poland naua fa jamhuriyyar Czech da kuma Switzerland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.