Isa ga babban shafi

Girgizar kasa mai karfin maki 5.7 ta afku a babban tsibirin Java

Hukumar binciken yanayin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasa mai karfin maki 5.7 ta afku a babban tsibirin Java na kasar Indonesia a yau asabar, kasa da mako biyu bayan wata girgizar kasar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 330.

girgizar kasa mai karfin maki 5.7 ta afku a babban tsibirin Java
girgizar kasa mai karfin maki 5.7 ta afku a babban tsibirin Java AP - Tatan Syuflana
Talla

Girgizar kasar ta afku a kasa mai nisan kilomita 112.5 (mil 70) kuma girgizar ta afku a nisan kilomita 18 kudu maso gabas da birnin Java na yammacin kasar.

Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka ko barna.

Hukumar kula da yanayi ta kasar ta ba da ma'aunin girgizar kasar mai maki 6.4, wanda kuma ya girgiza gine-gine a Jakarta babban birnin kasar.

Amma babu wata barazanar tsunami, in ji hukumar.

Indonesiya na fuskantar yawan girgizar ƙasa a matsayinta na kasa da ke kan zoben wuta ko  Ring of Fire na Pacific.

A watan da ya gabata wata girgizar kasa mai karfin awo 5.6 ta afku a garin Cianjur da ke yammacin Java, inda ta kashe mutane 331, tare da raunata dubun dubatar mutane, bayan da ya ruguje gine-gine tare da janyo zabtarewar kasa.

Mutane da dama ne suka samu kan su karkashin baraguzan kwanaki bayan girgizar kasar, inda aka samu nasarar ceto wasu da dama, ciki har da aikin ceto wani yaro dan shekara shida, wanda jami'an agajin gaggawa suka bayyana a matsayin abin al'ajabi.

Girgizar kasa mai karfin awo 6.2 da ta afku a tsibirin Sulawesi a watan Janairun shekarar da ta gabata ta kashe mutane sama da 100 tare da yin barna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.