Isa ga babban shafi
Indonesia

'Yan sandan Indonesia sun dakile shirin kai harin ta'addanci

‘Yan sandan Indonesia sun bankado asirin kungiyar masu tsattsauran ra'ayin da ta kai mummunan harin bam a Bali a 2002, na shirin kai wani sabon farmakin a yayin bukukuwan ranar samun 'yancin kan kasar a wannan makon.

Wasu 'yan sandan kasar Indonesia.
Wasu 'yan sandan kasar Indonesia. © Antara Foto/Novrian Arbi/ via REUTERS
Talla

‘Yan sandan musamman masu yaki da 'yan ta'adda na Indonesian sun samu nasarar kame mutane akalla 53 da ake zargi masu tsattsauran ra'ayi a larduna goma sha biyu da ke fadin kasar makon da ya gabata.

Wasu daga cikin wadanda ake zargin kuma sun tabbatar da cewa kungiyar tasu ta Jema’ah al Islamiyah ta kai harin harin Bali na 2002,  tana shirin kai wani harin yayin hutun ranar samun 'yancin kai na kasar ta Indonesia a farkon wannan makon.

tun kusan shekaru 20 da suka gabata ne dai, hukumomin tsaron Indonesia suka tarwatsa kungiyar Jema’ah Islamiyya bayan harin bama -baman da suka kashe mutane fiye da 200 a wurin shakatawar da ke tsibirin Bali.

Sai dai bincike ya bankado cewar kungiyar tana sake ginuwa, yayin da kuma aka saki jagoranta Abubakar Bashir daga kurkuku a wannan shekara bayan ya shafe lokaci a gidan Yari kan laifukan ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.