Isa ga babban shafi
Thailand

An gano mutumin da ya kai harin Bam a Bangkok

Gwamnatin kasar Thailand ta bayyana cewa ta gano wani mutun da ake zargi da hannu a harin Bam din da ya kashe mutane 21 a jiya litinin a wani wurin Ibada dake Bangkok, yayin da ta bayyana harin a matsayin mafi muni da aka taba kaddamar wa a Kasar.

Masu aikin ceto na kwaso gawarwaki a wurin da aka kai harin.
Masu aikin ceto na kwaso gawarwaki a wurin da aka kai harin. REUTERS/Kerek Wongsa
Talla

A cewar gwamantin, ta gano mutumin ne ta hotan bidiyon da na’urar da aka sanya akan hanya ta dauka, kuma ana farautar sa yanzu haka.

Firaministan kasar Prayut Chan-O-Cha, ya bayyana wa taron maneman labarai cewa suna neman mutumin kuma suna zaton yana daga cikin masu adawa da gwamnatin kasar a Arewa maso gabashin Thailand.

Hoton bidiyon wanda jami’an ‘Yan Sanda suka fitar ya nuna wani matashi sanye da karamar riga ruwar dorawa, dauke da jaga a kafadarsa na kai kawo kusa da wurin Ibadan kuma bayan wani dan lokaci ya fice ba tare da jakar ba kamar yadda hotan bidiyon ya nuna.

Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar 'yan kasashen ketere da ya hada da China da Hong kong da Singpore da Indonesia harma da Malaysia kuma kimanin mutane 100 ne suka samu raunuka.

Tuni dai Gwamantin Kasar ta yi allawadai da harin, wadda ta bayyana a matsayin mafi muni da aka taba kaiwa a Kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.