Isa ga babban shafi

Fashewar Bam a wajen Ibada ya hallaka mutane a Bangkok

‘Yan sanda a birnin Bangkok na kasar Thailand sun tabbatar da mutuwar mutuane 16 sakamakon wata fashewar bam da ya faru a wajen wani wurin ibada da ke birnin a yau litinin.Wasu ma’aikatan ceto da suka bukaci a sakaya sunan su sun ce tabbasa  Bam ne ya fashe kuma akwai mutane sama da 80 da suka samu rauninka.

AIDAN JONES / AFP
Talla

Shugaban rundunar ‘yan sandan kasar Chakthip Chijinda, ya ta ce ko baya ga mutanen 16 da suka mutu, akwai wasu da dama da suka samu raunuka.

Fashewar ya faru ne a lokacin da mutane ke gudanar da ibadar su, kuma wurine da baki ‘yan yawon bude ido ke kai ziyara, daga cikin wanda suka mutu hada ‘yan kasar China da Phillipines.

Tuni dai aka killace idan abin ya faru, kuma ana kan binciken yadda lamarin ya faru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.