Sojoji sun karbe gwamnati a Thailand
Babban Kwamandan rundunar Sojin kasar Thailand Prayut Chan-O-Cha ya bayar da sanarwar karbe gwamnati a kafar Telebijin din kasar bayan kwashe watanni Thailand na cikin rudanin siyasa. Kwamandan na Soji ya yace sun karbe mulki ne domin daidaita al’amurra a kasar.
Wallafawa ranar:
Akwai ganawa da Shugaban rundunar sojan kasar ya gudanar tare da shugabannin ‘yan siyasar kasar da ba sa ga maciji da juna, Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara amfani da wata dokar soja, da nufin hana barkewar tashe tashen hankula a kasar.
Rikicin siyasan kasar ta Thailand na afkuwa ne tsakanin gidan sarautar Bangkok da masu goya musu baya a bangare daya, da iyalan tsohon Firaminista Thaksin Shinawatra, attajirai da ke matukan samun goyon bayan al’ummar arewacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu